Taron Bitar Masu Ruwa da Tsaki

An gudanar da taron bitar masu ruwa da tsaki na shirin aikin yaki da cin hanci da rashawa a ranar 29 ga watan Nuwamba na 2018, a otel din Immaculate Suites and Apartments, Lamba 110 titin Adetokunbo Ademola Crescent, Wuse 2 - Abuja. Taron ya samu halartar mutane 36 daga jihohi 8: 9 daga Kano, 2 daga Niger, 2 daga Benue, 2 daga Filato, 1 daga Gombe, 1 daga Borno, 1 daga Nasarawa, 1 daga Jigawa da 17 daga Abuja. Takwas daga cikin mahalartan mata ne, yayin da ashirin da takwas maza ne. Har ila yau, mahalarta taron sun hada da jami'an gwamnati, shugabannin al'umma, kungiyoyi na gida (gami da sauran masu ba da gudummawar MacArthur) wadanda ke aiki kan sha’anin shugabanci nagari da kuma yaki da cin hanci da rashawa, da wakilan masu ba da tallafi don daidaita tsarin ayyukan, gano iyakokin yin canji, bayar da fifiko kan bukatu, da kuma shirya alamun nasara.

×