Madubi Shirin Rediyo na Yaki da Cin HAnci da Rashawa

Madubi, shiri ne na yaki da cin hanci da rashawa ne na rediyo mai tsawon minti 30 wanda ya dogara kacokan kan tattauna matsaloli da yanaye-yanaye da kuma kawo shawarwari kan abubuwan da ke shafar yaki da cin hanci da rashawa a Arewacin Najeriya. Shirin yana dauke da sashen wasan kwaikwayo wanda ke nusarwa kan batutuwan da suka shafi makamashin wutar lantarki da ilimi.

×