Jerin Wasan kwaikwayon Dadin Kowa na Yaki da Cin Hanci Da Rashawa

A watan Satumba na 2018 Equal Access ta kirkiri labaran wasan kwaikwayo 10 wanda aka mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa a cikin jerin wasan kwaikwayo na Dadin Kowa. An mayar da fifiko gurin nuna labaran cin hanci da rashawa/yaki da cin hanci da rashawa a fannin makamashin wutar lantarki da ilimi cikin jerin kashi 10 na wasan kwaikwayon da ya ciyo lambar yabo watau Dadin Kowa. Shirin ya shafi lamuran zamantakewa da suka shafi cin hanci da rashawa, da shan muggan kwayoyi, rikici cikin gida, ilimin yara mata, aikatau na yara, tashin hankali da fataucin mutane. An shigar da labarun ne na yaki da cin hanci da rashawa a cikin jerin wasan kwaikwayon ta hanyar amfani da jaruman da ake da su a cikin wasan, kuma a ka cakuda su tare da sauran labaran da yan jaruman wasan da ake nunawa a kowane wasan na mako-mako mai tsawo awa guda. An nuna labaran yaki da cin hanci da rashawa ne a cikin kashi na 24 zuwa na 73 na jerin wasan kwaikwayon Dadin Kowa.

A cikin wasan kwaikwayon AREWA24 na mako-mako mai dogon zango, watau Dadin Kowa, labaran yaki da cin hanci da rashawa a fannanin makamashin wutar lantarki da ilimi zasu ci gaba da taka rawa a lokuta na gaba. (Lura: AREWA24 ta sa ran hada gwiwa da masu ba da tallafin da kuma mashawartansu a kan yaki da cin hanci da rashawa, don kokarin gano wuraren da za a samu hanyoyin samar da sabbin labarai yayin da ake cikin kakar.

A bangaren makamashin wutar lantarki, Kawu Mala yana fama da matsalar rashin kudin da zai biya taransafomar da ya satay a biya kudin kula da lafiyar ‘yar sa, yayin da kuma yake fuskantar adawa daga abokan aikin sa, wadanda suke zargin rashin gaskiyar sa. Shin ya fi kowa jajircewa wajen aiwatar da aikinsa na farfado da tsarin wutar lantarkin? ko kuwa zai mika wuya ga wannan matsin lambar da yake ciki? Shin MD na kamfanin wutar lantarkin, wanda ya ba Kawu Mala damar biyan kudin taransafomar da ya sata maimakon ya kore shi, yanzu zai koma ya kawar da cin hanci da rashawa a cikin tsarin ta hanyar amfani da Kawu Mala a matsayin makusancinsa? Daga cikin wasu abubuwa, kamfanin wutar lantarki ya yi alƙawarin yin amfani da mita mai kati, kuma ga shi Kawu Mala ya ingiza ‘yan tawagarsa kan su yi tallan sabbin na’urorin, wanda a hankali-a hanakali mutane suna karba, wanda bada dadewa aka fara ganin fa’idar abun. A hankali a hankali, wasu daga cikin jama'a suka fara ganin alfanun biyan kudin wutar lantarki da suke tsammanin za su samu.

Duk dayake Kawu Mala ya ci gaba da fuskantar kalubalen dake gabansa na shan kwayoyin 'yarsa, da kiwon lafiya, ya riƙe mutuncinsa, kuma ya ci gaba da jagorantar gwagwarmayar kawar da cin hanci da rashawa a tsakanin ma'aikatan kamfanin wutar lantarkin. Akwai jinkirin ci gaba, kuma akwai matsaloli da yawa, amma ya ci gaba da dagewa.

A labarin fannin ilimi kuwa, kasancewar Dakta Amina ta fahimci abin da ta gano game da cin hanci da rashawa a tsakanin malaman makarantar su Bintalo da shugabar makarantar yana ci gaba. Kwamishinan Ilimi ya dauko sabon shugaban da ke da ra'ayin kawo canji don tafiyar da makarantar, amma sabon manajan yana fuskantar tawaye a tsakanin wasu malamai da ma'aikatan da ke adawa da canjin, kuma ba sa son su hakura su daina rabon abubuwan da suka samu daga cin hancin da rasahawa. A halin da ake ciki, tare samun goyon bayan Dakta Amina akai-akai, Bintalo ta ci gaba da karatun ta duk da kalubalen da take fuskanta daga wajen mahaifinta, Mal. Kabiru, wanda ba ya tunanin kowa sai kansa, kuma baya baiwa komai daraja fiye da nairar da ya roƙo ya jefa a aljihu.

Dokta Amina ta fahimci cewa cin hanci da rashawa a makarantar yayi kamari sosai, kuma za a bukaci dagiya koyaushe ta hanyar ɗalibai, iyaye, da jagorancin al'umma don samun gyara.

A tsawon shekara, shirin Dadin Kowa zai iya amfani da tsoffin jaruman wasan, da kuma ‘yan wasu sabbi, don bincikar adadin wasu gurare na cin hanci da rashawa tsakanin al’umma da ya zarce na ilimin makarantar firamare da fannin wutar lantarki, gami da barnar da ake yi a asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya, da na 'yan sanda, da makarantun sakandare da jami'o'i, da guraren aikin al’umma da kuma kotuna.

Baya cin hanci da rashawa a waɗannan fannoni na jama'a, Dadin Kowa zai kuma yi duba don bincikar ire-iren waɗannan matsaloli dake tsakanin iyalai da kuma tsakanin makusanta wata al'umma, wanda ya riga ya zama ruwan dare a Najeriya.

Daga qarshe, jerin wasan kwaikwayon yana da damar da zai shigo da masu sauraro ciki don gina wata amintacciyar tattaunawa wacce zata kai su ga yin tunani, kuma mai yiwuwa ne su rungumi akida wadda zata sa su yarda cewa “canji yana farawa ne daga kowanne mutum” ma'ana kowane mutum ya kasance mai son sauya tunaninsa game da cin hanci da rashawa, kafin ya fara yunƙurin canza wasu, ko yunkurin sake fasalin gwamnati da wasu cibiyoyi.

×