“Cost of Corruption" GASAR FINA_FINAI

A watan Nuwamba 2018 Equal Access ta kaddamar da gasar fina-finai domin kananan masu shiryawa da masu bada umarni masu tasowa daga masana’antar Kannywood ko Nollywood da kuma sauran yankunan Najeriya. An yada sanarwar gasar fina-finan a kafofin sada zumunta da kuma shafin yanar gizo na Equal Access Najeriya. Babban makasudin yin gasar shine a sami ra'ayoyin fina-finai wanda suka mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma hanyoyin kawar da ita daga Najeriya. A lokacin da aka kusa rufe daukar masu shiga a watan Janeru 2019, an samu masu takardun masu neman shiga arba’in da uku (43) ta yanar gizo da kuma takardun hannu, an kuma zabi mahalarta goma sha biyar (15) don halartar gasar shirya fina-finan a Abuja wanda aka gudanar daga 4 zuwa 8 ga watan Fabrairu 2019. Gasar ta samu alkalan da suka yanke hukunci da suka hada da: - Farfesa Alemika Etannabi – Farfesa Tor Iorapuu – Farfesa Christiana Best – Bem Pever. A karshe gasar fina-finan, masu shirya shiri hudu ne sukayi nasara, wandanda suka shirya fina-finai masu take da kuma dauke da sakonni kan yaki da cin hanci da rashawa a fannonin makamashin wutar lantarki da ilimi a Najeriya. Su ne Dimbo Atiya (THREEBULATIONS) Ishaiku Gumut (INTEGER) Tijani Shehu (Dan Kasa) Yusuf Elhaj (Ali Baba)

×