Sashen Shirin Gari Ya Waye

AREWA24 tana gabatar da wani sashen shiri da yake bunkasa jerin wasan kwaikwayo na Kwana Casa’in da kuma shirin dake nuna yaki da cin hanci da rashawa na Dadin Kowa cikin shaharren shiri mai zuwa a kullum na Gari Ya Waye. Shirin ya hada da gamayyar labaran bayan fagge a yayin da ake gudanar da shirin, da kuma tattaunawa tare da manya-manyan jarumai da marubuta da masu bada umarni da kuma sauran wadanda suke da alaka da aikin.

×