Karfafawa Kafofin Yada Labarai don Muhimmancin Matakan Al'ummma A Najeriya (SMS-CAM)

Duba da irin mu’amala mai zurfi tsakanin al’umma da kuma kwarewa a kafar watsa labarai a duk fadin yanki, Equal Access International tayi fice wajen tallafawa manufofin Gidauniyar Mac Arthur gurin taimakawa da kuma matakan daukar nauyi, tsage gaskiya da kuma shugabanci na gari a Najeriya.

Wadanda Su ka Assasa

Gidauniyar MacArthur tana goyon bayan mutane masu basira da kuma cibiyoyi masu tasiri da suka sadaukar da kai wajen samar da karin wadatacciyar rayuwa ta zaman lafiya. Karin game da zaben jakadun MacArthur, TMF na aiki don kare hakkokin dan adam, ci gaban kiyaye duniya da tsaro, mayar da birane da gurare masu kyau, da kuma fahimtar yadda fasaha take illata yara da al’umm.

Adadin Lokaci

2018- 2021

Ayyuka

Binciken Farko kan Aikin SMS CAM

An baiwa Dakta Henry Gyang Mang mai bada shawarwari kwangila a watan Oktoba na 2018 don tsarawa, da aiwatarwa, da yin nazari da kuma fitar da rahoto game da ra’ayoyin jama'a kan matakan yaki da cin hanci da rashawa a cikin manya-manyan jihohi biyar na Gombe, Kano, Borno, Niger da Plateau.

Wasan Kwaikwayon Kwana Casa'in (Kashi 90)

Equal Access Nijeriya tare da hadin gwiwar Arewa24 sun samar da kuma gabatar da shirye-shirye guda goma sha uku (13) na jerin wasan kwaikwayon Kwana Casa'in a matsayin wani bangare na ayyukan gidauniyar MacArthur.

Wasan Kwaikwayon Kwana Casa'in (Kashi Na 90)

A karshen zangon 13 na sassan 90 jerin wasan kwaikwayon Kwana Casa’in, an zabi dan fafutukar yaki da cin hanci da rashawa watau Malam Adamu a matsayin gwamnan kirkirarriyar jihar Babawa ta Arewacin Najeriya. Ya hau gadon mulki cikin rudani, mai cike da cin hanci da rashawa ga kuma rashin adalci. Don ya kiyaye alƙawarin da ya dauka na gudanar da mulki na gaskiya da shugabancin da zai yiwa jama’a aiki, tilas ne ya yi watsi da bukatun magoya bayansa waɗanda ke tsammanin za a biya su ladan goyon bayan da sukayi na taimaka masa a ka zaɓe shi, kamar yadda kuma jam’iyyar ‘yan adawa da suka lashi takobin kawo mishi cikas a duk kokarinsa. Sabon gwamnan zai gano cewa kawo karshen cin hanci da rashawa a gwamnati da duk fadin jihar, abu ne mai saukin fada a baka ba a aikace ba.   

Shirin Gari Ya Waye

Tashar talabijin ta AREWA24 tana watsa shiri wadanda suke bunkasa shirye-shiryen wasannin kwaikwayo na Kwana Casa'in da kuma mai dauke da labarin yaki da cin hanci da rashawa watau Dadin Kowa a shararren shirin nan mai zuwa kowacce rana, watau, Gari Ya Waye.

Taron Bitar Masu Ruwa Da Tsaki

Taron ya tattara jami'an gwamnati, da kungiyoyin cikin gida wadanda ke aiki kan sha'anin shugabanci nagari da kuma yaki da cin hanci da rashawa, da wakilan masu ba da tallafi don daidaita ayyuka, da gano iyakokin canzawa, fifitawa kan bukatu, da tsara alamun nasara.

Dadin Kowa Labarin Yaki da Cin Hanci da Rashawa

Sassan wasan kwaikwayo na Dadin Kowa na labarin Cin hanci da rashawa ne / Yaki da cin hanci da rashawa a fannin ilimi da na wutan lantarki wanda aka riga aka gabatar dasu musamman a cikin bangarori goma, (10) a jere cikin wasan kwaikwayon da ya ciyo lambobin yabo na AREWA24. Shirin ya yi maganin lamuran zamantakewa da suka shafi cin hanci da rashawa, da shan muggan kwayoyi, rikce-rikice, ilimin yara mata, bautar da yara, ta’addanci da fataucin mutane.

“Cost of Corruption" GASAR FINA_FINAI

A watan Nuwamba 2018 Equal Access ta kaddamar da gasar fina-finai domin kananan masu shiryawa da masu bada umarni masu tasowa daga masana’antar Kannywood ko Nollywood da kuma sauran yankunan Najeriya. An yada sanarwar gasar fina-finan a kafofin sada zumunta da kuma shafin yanar gizo na Equal Access Najeriya. Babban makasudin yin gasar shine a sami ra'ayoyin fina-finai wanda suka mayar da hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma hanyoyin kawar da ita daga Najeriya.  

LATSA:

kano, kaduna, maiduguri, sokoto, kebbi, zamfara, nassarawa,
plateau, kogi, abuja gombe, niger, & taraba.

ABOKAN AIKIN JARIDA:

×