Haihuwar Sabon Jariri da kuma
Shirin Lafiyar Yara (MNCH2)

Shirin haihuwar sabon jariri da Lafiyar Yara (MNCHXNUMX) shiri ne wanda Ma'aikatar cigaban kasa da kasa ke tallafawa akai daga Gwamnatin Burtaniya. Wannan aikin kula da lafiya ne a fadin jihohi shida na arewacin Najeriya, na tsawon shekaru biyar. Manufar aikin shine samar da ingantacciyar kulawa mai dorewa daga daukar ciki har izuwa shekaru biyar na farkon rayuwar yaro, don rage mutuwar mata da jarirai. Bugu da kari, don yin aiki tare da sauran ƙungiyoyi na al'umma da malaman aikin lafiya don cimma burin ta na inganta rayuwar yara, mata da na iyalai. Equal Access ta samar da tallace-tallace da wakoki wadanda suke karfafawa mata gwiwar neman ingantaccen kiwon lafiya a matakin farko a duk fadin Arewacin Najeriya.


MNCH2 ta baiwa Equal Access tallafi na tsawon watanni 3 cikin shekara ta 2018. Shiri ne na rediyo don inganta lafiyar Mata masu haihuwa a arewacin Najeriya. MNCH 2 ta yi amfani da kusancin da EAI take da shi na tashoshin rediyo na cikin gida wajen cimma burinta.

Nasarori da Muhimman Abubuwa na Gaba:

EAKDI ta fitar da jerin sanarwa ga jama'a watau (PSAs) da wakokin jan hankali ga MNCH 2 a tsakiyar shekara ta 2018, kuma tana rarraba shirye-shiryenta ga gidajen rediyoyin da ake hulda da su guda takwas a Arewacin Najeriya.

EAKDI zata ci gaba da yin aiki da aiwatar da duk wasu aiyuka a Najeriya dake hannu, kuma zata dage wajen hada gwiwa da hukumomin gwamnati, da hukumomin dake da danganta, kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida, masana na Najeriya da kungiyoyin fararen hula. Tana bayar da horon kwarewa ga dukkan ma'aikata, da kungiyoyin hadin gwiwa, mahalarta da masu sa kai. Bugu da kari kuma tana haɓaka shawarar aiwatar da aiki waɗanda suka dace da dabarun ci gaban Najeriya, musamman a fannonin da tafi ƙwarewa; dakile ta'addancin tsatstsauran ra’ayi, samar da wasu labarai na daban wadanda suke yiwa raunanan kungiyoyi rigakafi, kokarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma tallafawa kiwon lafiyar uwa da yara.  

Farar Tattabara Logo
×