Taron Bitar Masu Ruwa da Tsaki

A ranar 4th ga watan Afirilu shekarata 2019, aka gudanar da taron bitar masu ruwa da tsaki a otel din Babale dake Kano. An samu halartar mutane 21 cikin 26 da aka gayyata; 20 daga jihar Kano sai kuma 1 daga jihar Filato. Mahalarta mata 10 ne da kuma maza 11.

Wasu daga cikin manyan masu ruwa da tsaki wadanda suka halarci taron sun hada da: Wakili daga wani kamfanin sadarwa, Mace mai fafutuka, Shugabar gargajiya, Malamin addinin Islama mai sassaucin ra'ayi, Mataimakin daraktan CITAD, Darektan mata, Ma’aikatar Harkokin Mata, Masanin halayyar dan-Adam da na jinsi. , Malaman FGD, Wani tsohon kwamishina daga Ma'aikatar Kimiyya da Fasaha.

Makasudin yin bitar shine a samu musayar ilimi da shawarwari tare da mahalarta a game da manufofin aikin Fasaha a Rayuwar Iyali, da gabatar da sakamako na baya daga tawagar tattaunawa ta fahimta, da samun karin bayanai kan matsalolin da suke yiwa mata tarnaki wajen samun damar amfani da fasaha cikin Kano da kewayenta; neman tallafi da kuma yardar al'umma kan manufofin aikin da hanyoyin tunkara - gami da samo abokan huldar yin aikin da kuma fahimtar waye yake aiki akan wannan batun; gaskiyar abin da muke fahimta a game da banbancin jinsi kan amfani da fasaha a arewacin Najeriya, da kuma karɓar ƙarin shawarwari kan aikin da kuma tsarin shirye-shiryen rediyon. An fuskanci yiwuwar shigo da tsarin SHW wajen ganin kasancewar sa da kuma amfani shi inda hali. A haka dai, a wannan ranar aka kammala tattaunawar da Tambayoyi da Amsoshi da kuma rarraba kungiyoyi. An kai ga muhimmin mataki na mu’amala da kuma kyakkyawan sakamako daga wajen mahalarta.

Taron ya baiwa tawagar damar ta tantance abubuwan da aka samo da kuma kara samun haske daga ginanan bincike tare da wani mai sauraren. Dukkanin mahalartan sun amince da binciken farko na FGD kuma sun ji a ransu EAI tayi aiki mai kyau wajen binciken. Kusan dukkan mahalarta taron sun fahimci cewa bangaren iyali shine babban cikas ga mata wajen amfani da fasaha da yanar gizo da kuma cewa kara yin bincike kan wannan lamari ya na da matukar muhimmanci. Daya daga cikin takaicewar da suka yi nuni akai shine tsarin yin binciken, sun nuna cewa kungiyoyin 8 na FGD mai dauke da mutane 80 kacal da kuma IDI 20 yayi karanci sosai ya nuna ainhin gaskiyar abinda yake wakana kan mutane miliyar 11 da doriya a cikin jihar Kano.  

×