Tattaunawa ta Fahimta (FGD)

A XNUMX da kuma XNUMX ga watan Fabrairu XNUMX, Equal Access International ta kaddamar da wani kwakkwaran bincike, wanda ya kunshi Kungiyoyin Tattaunawa ta Fahimta watau (FGD) su XNUMX wanda aka gudanar a jihar Kano, Arewacin Najeriya, a matsayin wani ɓangare na ayyukan bincike mai zurfi. Manufar FGD shine a samar da kyakkyawar fahimta game da al'adun al'umma, wanda ya hada da tsarin dabi'un daidaikun mutune da kuma akida ta addini akan yadda mata da yammata suke samun damar amfani da fasaha. Tattaunawar ta kuma nemi ta gano takamaiman bayanai a game da irin nau'in fasahar da mata da 'yan mata ke iya samun damar amfani da, wane irin cikas suke fuskanta, sannan kuma wane irin makamancin cikas aka samu tsakanin mahalarta bitan. A tare da FGD akwai wani tebirin bibiyar rubuce-rubuce akan amfani da wayar hannu tsakanin mata da yammata, tare da wata ganawa mai zurfi da aka ware. Teburin bibiyar da binciken da aka gudanar shi zai bayyana shirin Fasaha a Rayuwar Iyali, Tawagar Koyo da Tattaunawa da kuma Aiwatarwa watau (LDAG), jerin shirye-shiryen rediyo gami da tsarin karatun dijital.

Tawagar Tattaunawa Ta Fahimta

Kungiyoyin guda 8, suna kunshe da masu bada amsa 10 waɗanda suka haɗa nau'ikan shekaru huɗu (4); Shekaru 13-17, shekaru 18-25, shekaru 26-35, sai kuma shekaru 36 – 50. Dukkanin masu bada amsar sun kasance masu ba da gudummawa ne, sannan sun fito ne daga jihohi goma sha tara (19) na arewacin Najeriya kuma dukkansu mazauna cikin Kano ne a halin yanzu. Ga kowane gungu na FGD, inda aka zaɓi mahalartan da suka dace wanda ya hada daidaikun mutane daga mabanbantan al'adu da tattalin arziki, waɗanda su ka kasance masu zaman kansu, ko ma’aikatan al’umma ko dalibai da dai sauran su. Duk yan kungiyoyin shekarunsu sun daidaita kuma kowanne jinsi a ware suke. Binciken ya bankado muhimman dalilai da yawa, wadanda suke karfafawa abubuwan da suke kawo tarnaki don kawo sauyi da kuma maye gurbin babban abinda yake kawowa mata da yammata cikas wajen samun damar amfani da fasaha.

×