Taron Tawagar Ba da Shawarwarin Shirye-shirye (CAG)

Taron Tawagar Bada Shawarwarin Shirye-shirye watau (CAG) na Fasaha A Rayuwar Iyali an gudanar da shi ne a ranar XNUMX ga watan Agusta XNUMX a ofishin EAI Nijeriya dake Kano. Makasudin yin taron CAG na farko shine, don a yiwa mambobin CAG bayanin manufofi da burin wannan aikin, a bayyana musu irin rawar da zasu taka da aiyukansu a matsayinsu na mambobin CAG, sannan a kuma basu wata dama da zasu bibiyi shirin rediyo na Fasaha A Rayuwar Iyali na farko. Duk da cewa tawagar ta masu ba da shawarar ba kwamitin bincike bane, amma suna da muhimmiyar rawar takawa ta tabbatar da inganci da kuma dacewar shirin na rediyo (Fasaha A Rayuwar Iyali), su ba da shawarwari kan batutuwan da za a tattauna akai, amsoshin masu sauraron shirye-shiryen da a ka riga a ka watsa, da kuma karin haske kan kowanne irin kutse ko kuma kayayyakin aiyukan da zasu tabbatar da shirin ya na yin abinda ake bukata da kuma yin tasiri. Mambobin CAG suna damuwa wajen tabbatar da cewa shirin ya kunshi al’adu kuma zai dace da abubuwan da zasu dakile tsangwama, da kuma tabbatar da cewa yana da saukin fahimta ga iyalai da kuma al’umma gabaki daya.

A karshen taron, mambobin CAG sun samu kyakkyawar fahimta game da irin nauyin da ya rataya a wuyan su, da kuma shawarwari da abubuwan lura da aka gabatar a lokacin taron, wanda EAI zata aiwatar duk inda ya dace.

×