Horon Masu Rahotanni na Al'umma

A ranakun 4 da 5 na watan Satumba na shekarar 2018 aka baiwa Masu Kawo Rahoton Al’umma watau (CR) horo a cikin Kano, a Otel din Chilla Luxury. Wanda aka samu adadin mahalarta 35 tare da CR 16 da kuma sabbin masu hada kan al’umma 19. 6 daga cikin mahalartan mata ne alhalin 29 maza ne. Dukkan mahalartan sun fito ne daga duk jihohin Arewacin Najeriya irin su Kano, Jigawa, Katsina, Borno, Gombe, Bauchi, Yobe, Taraba, Adamawa, Plateau, Kebbi, Sokoto, Nasarawa, Abuja, Kaduna, Zamfara da Niger.

Babban makasudin horar da 'yan rahotan da masu hada kan al’umma shine don a kara inganta karfin su wajen Dakile Tsautstsauran Ra’ayi da jagorancin al'umma tare da basu horo su kasance masu gudanar da nasihohi mai tasiri sannan kuma su dinga isar da sakonni a cikin mabanbantan al’ummomin su. Ga wasu hotuna a kasa na wajen taron bitar. 

×