Zangon Hotuna na EAI-NATGEO

Equal Access International (EAI) ta gudanar da wani zangon Hotuna a Kano, Najeriya. Tun daga XNUMX zuwa XNUMX ga watan Nuwamba XNUMX, domin bada gudummawa ga irin kwazon aikin shahararriyar cibiyar nan National Geography ta duniya watau (NG), wanda suka ƙwarance wajen daukar hotuna da tacewa, sune suke jagorantar sansanonin hotuna a duk faɗin duniyar nan. An horar da mahalarta kan koyan aikin jarida, bayar da labarai, daukar hoto na dijital da na manyan wayoyi, aikin jarida na hotuna, kirkirar kamfen din kafofin sada zumunta, hanyoyin tsarin ci gaban matasa da kuma magance tsattsauran ra'ayi, hanyoyin bada labarai, da hanyoyin karfafa gwiwa na EAI.

EAI-Nigeria ta yi tallatar ta hanyoyi daban-daban don yin kira mahalarta su samu shiga. Kiran yana baiwa shigar matasa fifiko waɗanda ba taba shiga cikin ayyukan EAI na baya ba. An karɓi adadin masu san shiga ɗari hudu da tamanin da hudu (484), an tantance. An yiwa wadanda aka fitar da sunayen su tambayoyi, an sake fitar da mutun ashirin (20) daga ƙarshe. 

BURI /MANUFOFIN AIKIN

Shirin Wanzar da zaman lafiya, wanda Equal Access International (EAI) ke aiwatarwa, tare da hadin gwiwar National Geographic watau (NG), zata horar ta kuma jan hankalin matasan Arewacin Najeriya da su kasance jajirtattun 'yan kasa, masu bayyana labarai a hotuna, da kuma wanzar da zaman lafiya. Ta hanyar tsarin koyarwa da bada horo na kwanaki 5 na gwaji da kuma samar da jakadu, matasa 20 sun karu da daukar hotuna, kafofin watsa labarai na dijital, da dabarun bayar da labarai, wanda zasu yi amfani da su don magance matsalolin zamantakewar al'umma wanda galibi yakan haifar da tashe-tashen hankula da ta'addanci, kuma zai kara fadada muryoyin da ba a jiyo su da kuma kyawawan labaran da za su iya canza halaye, dabi’u, da kuma yanayin zamantakewa ta hanyar kamfen, labarai a hotuna, labarun dijital, da ayyukan inganta zaman lafiya. Ta hanyar kutsawa cikin hanyoyin kafofin watsa labarai na EAI da cibiyoyin sadarwa, za a sada matasa da wadatattun tashoshin da zasu bunkasa kwarewar da suke da ita da wannan dama da suka samu don inganta dabarun su da kuma fadada hangen su akan al’umomin su.

Hoto da kafofin watsa labaru suna cikin manya-manyan makaman yaki, dukkansu hanyoyin tayar da hankali ne kuma kayayyaki ne na wanzar da zaman lafiya. Tarihin baya-bayan nan ya isa ya ba mu misalai da yawa, irin mahimmancin rediyo wajen ƙara hura wutar tashin hankali a kisan kare dangi na kasar Rwanda da karfin ISIS da Boko Haram na ɗaukar yan kungiya da tsageranci da hotuna na tursasawa da bidiyo da kiraye-kiraye na canjin zamantakewar al'umma ta hanyar tashin hankali. Bayan shekaru goma na shirye-shiryen, CVE ya kasance yafi mayar da hankali kan sababi da korafe-korafe, kuma sau da yawa ba su da ƙarfi daidai da labaran tursasawa da kirkirarrun hangen nesa waɗanda zasu yi hamayya daidai da girma da fadi da na yan kungiyar ta’addanci kuma suna iya tattaro keɓaɓɓun kuma kaskantattun matasa don samar da kyakkywan canji jama'a. Ci gaban fasaha da yawaitar damar amfani da talabijin, da kafofin watsa labarai, da ɗaukar hoto na dijital suna kara yawaitar kafofin watsa labarai na hotuna da suke zama kayan aikin da ba’a sani ba marar haɗari wanda galibi shahararru ne suke sarrafawa. Abin takaici, yawancin kungiyoyi a fadin duniyar nan suna ware kansu cikin tsari don samar da hotunan su da labaru kansu. Yayin da adadin hotunan tashe-tashen hankula suke ci gaba da karuwa, buƙatar yin cikakken bayani mai gamsarwa a hotuna ya zama tilas.

An kai karshen zangon hotunan a Kano da Baje Kolin Hotunan Al’umma (gami da rakiyar tallace-tallace na yanar gizo) wanda zai haɗa da bikin nune-nune da kuma tattaki. Wannan zai zama wata dama ce ga mahalarta Zangon Hotunan da zasu raba ayyukansu da hangen su tare da sauran al’umma. Za a nuna bikin a kafofin sada zumunta, kafar watsa labarai ta Farar Tattabara, za a kuma gayyato cibiyoyin watsa labarai na cikin gida don samun ƙarin yaduwar abun. Za a gayyaci daliban jami’a don kasancewa jakadun bayar da labari na dijital su kuma koma cikin al’umominsu kuma su ci gaba da aiyukansu na daukar hotuna, bayar da labarai da kuma wanzar da zaman lafiya. Jakadun zasu karbi manyan wayoyi mai dauke da na’urar daukar hoto mai karfi don ajiyewa da kuma ci gaba da sana’arsu a matsayin masu bayar da labarai na hotuna da kuma gwagwarmaya. Ci gaba da haɓaka fasaharsu kamar masu ba da labari da kuma masu ba da shawara. Har ila yau, jakadun zasu dinga samun kulawa akai-akai daga ma'aikatan EAI. A matsayin jakada, matasa za su ƙara samun damar taka rawa a matsayin masu canza halayya tsakanin al’umominsu kuma zasu shiga sahun jakadun EAI waɗanda ke Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. EAI za ta ba da ƙarin tallafi wanda ya hada da wayewa kan kafofin sada zumunta kan tsarin shahararren dandamalinta na Farar Tattabara. Bugu da kari, NG za ta nuna hotuna a baje koli na nan gaba da kuma shafukan hukumar na yanar gizo. Hakanan, za a raba hotuna tare da Ofishin Jakadancin Amurka don amfani da su a baje kolin su na gaba, da labarai, da kuma wallafe-wallafen su. 

Wanda su ka Halarta

Abubakar Mohammed

Abubakar Mohammed

Kaduna
Saminu Bitrus

Saminu Bitrus

Bauchi
Igebde Ogbole Umoru

Igebde Ogbole Umoru

Abuja
Usman Abba Zanna

Usman Abba Zanna

Borno
Umar Faruk Musa

Umar Faruk Musa

Kano
Hunokwaipwa Haziel Tonsan

Hunokwaipwa Haziel Tonsan

Adamawa
Kazeem Emeka Badmus

Kazeem Emeka Badmus

Jigawa
Muhammad Haruna Alhaji

Muhammad Haruna Alhaji

Yobe
Yau Alhaji Ahmed

Yau Alhaji Ahmed

Yobe
Abdulrashid Muhammad Gidado

Abdulrashid Muhammad Gidado

Taraba
Safiyya Ali-Daba

Safiyya Ali-Daba

Borno
Jubilee Anita

Jubilee Anita

Kogi
Vanessa Idoko

Vanessa Idoko

Benue
Zainab Ahmad Ahmad

Zainab Ahmad Ahmad

Kano
Nasfidon Nasara

Nasfidon Nasara

Adamawa
Regina Ojunogwa Alfa

Regina Ojunogwa Alfa

Kogi
Maryam Lerit Turaki

Maryam Lerit Turaki

Plateau
Maryamu Barnaba

Maryamu Barnaba

Gombe
Adamu Maryam Ndamudi

Adamu Maryam Ndamudi

Kaduna
Zulai Usman Salihu

Zulai Usman Salihu

Kano
×