EAI NIGERIA

MANUFA

EAI na taimaka wa al'ummomi a faɗin duniya su samu ci gaba mai ɗorewa da sauyi na canji ta hanyar ingantattun kafofin watsa labarai, da fasaha, da samfurin wayar da kai. Ta hanyar kirkirar mafita tare da al'umma, shirye-shiryenmu mallakar gida ne tare da la’akari da al'adun gargajiya. Muna gina yanayin sadarwa na zamantakewa wanda ya samo asali kuma ya bunkasa, da ƙirƙiro hanyoyin fitar da muryoyin wadanda aka ware, da gina ƙungiyoyi na cikin gida waɗanda ke kawo canji mai ƙarfi, masu kawo sauyi cikin al’adu da inganta kirkira, da kyawawan hanyoyin magance matsalolin rayuwa.

IMG_0828

"

"Ta hanyar sanya ingantattun labarukan mutane da bukatunsu a tsakiyar shirye-shiryenmu, jama’a da daukacin al'umma zasu canza labarukan su daga rashin-karfafawa da wariya izuwa karfafawa da kuma abu mai yuwuwa. "

Ronni Goldfarb

Mai kafa kuma memba na kwamitin

Tarihinmu:

Shugabannin Ci gaban Tunanin-Dan Adam na Kasa da Kasa

A shekara 2000 ne, Ronni Goldfarb tayi wani hangen nesa. Tare da irin saurin haɓakar bayanai da fasahar sadarwa da kuma irin karfin imanin daidaikun mutane na tasirin canji, ita da wata yar karamar ƙungiya ta mutane kaɗan suka ƙaddamar da Equal Access International watau (EAI.). An samar da EAI ne daga irin nauyin da aka dauka na samar da ci gaban dan adam da kuma ingantacciyar karfafawa ta hanyar Ka'idojin mutane na duniya - sauraro, tausayi, girmamawa, mutunci, koyo, kirkire-kirkire da bayar da labarai.

Tsakanin 2001 zuwa 2002, EAI ta samu tallafin Gidauniyar Ford da kuma tallafin Gidauniyar Majalisar Dinkin Duniya bi da bi. Wadannan kuɗaɗen, su suka ba da damar ƙaddamar da manya-manyan aiyukan ƙungiyar. Aiyukan namu ne suka shawo kan aikin rigakafin cuta mai karya garkuwar jiki da kuma na tallafin mata a kasar Nepal da shirye-shirye na zamantakewa da na ilimi ta hanyar amfani da tauraron dan adam zuwa garuruwan karkara 7,000 a fadin kasar Afghanistan. Ayyukan farko na EAI wanda ya haɗa da sauyin hallayya na zamantakewar jama'a, sadarwa da kuma mu’amala da al'umma ya sa muka sami babbar lambar yabo ta Tech Award a bangaren (Ilimi) saboda nasarar da aka samu a Nepal. Samun lambar yabo ta Tech a shekara ta 2003 ta tabbatar da cewa muna kan hanya gagarabadau kuma a shirye muke a gwada mu.

A karkashin jagorancin Ronni, EAI ta fadada a ciki da kuma kasashe goma na Asiya da Afirka. Kungiyar tana aiki ne don karfafawa mata da 'yan mata da kuma rigakafin tayar da hankulan su. Ta tallafa wajen ilmantar da miliyoyin matasa da aka ware tare da koya musu dabarun zaman rayuwa da horan sana’o’in rayuwa da habaka fara aikin wanzar da zaman lafiya a wasu daga cikin yankuna mafiya fama da kalubale a duniya.

Muhimman Al’amura:

Kirkirar Katafaren kamfani

A shekara ta 2014, EAI ta ƙaddamar da tashar talabijin ta farko mai gabatar da shirye-shiryenta a kyauta ba dare ba rana, cikin harshen Hausa zalla a tauraron dan adam. Wanda don ‘yan Arewacin Najeriya ake yi kuma suke shiryawa. AREWA24 (www.arewa24.com) ne suke gabatar da shirin da yake karfafawa matasa gwiwa, da ilmantar da yara, da tallafawa mata da 'yan mata, da bunkasa wanzar da zaman lafiya, da kuma bikin al'adun gargajiya da tarihin arewacin Najeriya. A shekara ta 2017, AREWA24 ta zama cikakkiyar tasha mai zaman kanta, ta sami babban mai hannun jari, kuma tana gunadar da aiyukanta ne da kudaden shigar da take samu.

Lambobin Yabo: EAI ta karbi lambobin yabo masu yawa, da suka hada da lambar yabo ta NASDAQ Technology Award a Masana'antar The Tech Museum for Innovation da ke San Jose, California; lambar yabo ta One World Media Award saboda aiyuka Muryoyi wanda yayi maganin matsalolin rikicin da ke tsakanin mata da cuta mai karya garkuwar jiki, da kuma shaharriyar lambaon yabo ta Microsoft Education a Masana'antar Tech Museum a shekara ta 2016.

A shekara ta 2018, EAI ta shirya don muhimmin ci gaba na fadadawa. Bayan shekaru 18, adadin yawan masu bibiyar shirye-shiryen da kungiyar take watsawa ya zarce fiye da mutane miliyan 200 tare da dauwammun masu sauraro da kallo fiye da miliyan 75, da kuma fiye da mutane 118,000 wanda kai tsaye sun riga sun shiga cikin ayyukan al'umma ta hanyar shirye-shirye masu matukar tasiri. A wannan matakin ne, a ka zabi Ronni don matsawa gaba, saboda EAI ta ci gaba da amfana da kokarinta na sadaukar da kai ta hanyar yin aiki a kwamitin Daraktoci kuma a matsayin babban Mai Bada Shawara. An zabi Mista Byron Radcliffe a matsayin sabon Shugaba & Babban Mukaddashin Shugaba don ya jagoranci EAI zuwa wani mataki na ci gaba.

"

"A ganina, ta'addanci yana samuwa ne sanadiyar rashin shugabanci na gari…. Rashin aikinyi ga matasa yana daya daga cikin muhimman dalilan da suke ingiza mutane izuwa tsageranci. Mafita shine a bunkasa tattaunawa da kuma warware rikice-rikice. "

PPF

memba

Equal Access na Alfaharin Yin Hulda da:

×