BARKA DA ZUWA SHAFIN

FARAR TATTABARA

Farar Tattabara cibiyace ta isar da sako na yanki, wanda aka mayar da hankali akan bunkasawa da kuma bada kariya ga jagoranci na matasa da kuma Dakile Tsatstsauran Ra’ayi (CVE), da Tsarin Inganta zaman lafiya da dabarun isar da sako a Arewacin Najeriya da yankin Sahara, inda ake amfani da harshen Hausa a matsayin muhimmi kuma matsakaiciin hanyar sadarwa. Equal Access International ta kaddamar da tsarin shirin Farar Tattabara...a shekara ta 2017 dauke da shirye-shiryen rediyo na asali guda uku, wanda sune:Ina Mafita, Ilimi Abin Nema da Labarin Aisha.

Farar Tattabara Logo

TARIHI

A shekara ta 2013 EAI ta fadada gagarumin aikinta akan CVE a cikin yankin sahara na Afirka don kafa tashar talabijin a harshen Hausa cikin Arewacin Najeriya wanda babu kamar ta, mai aiki kullum ba dare ba rana, watau AREWA24. Aikin da ya dauki tsawon shekaru yana baiwa ma’aikatan EAI na gida damar bunkasa tushe mai zurfi da kuma habaka karfinmu domin samar da kafofin yada labarai na kasuwanci wadanda suka kafu akan tushen canza zamantakewa da dabi’un sadarwa.

Yanzu AREWA24 ta yi nasarar samun lambar yabo, mallakin ‘yan gida, kuma kamfanin watsa shirye-shirye mai zaman kansa. A shekara ta 2016, EAI ta kafa Cibiyar Isar da Sako na yanki a karkashin shirin Farar Tattabara cikin harshen Hausa, domin karfafa gwiwa da manufofi da muryoyin matasa har da kuma al’umomi don dakile matsalolin zamantakewar al’umma, da halayya da dabi’u marasa kyau.

AYYUKANMU

Logo Arewa24

AREWA24: Tashar talabijin ta farko kan tauraron dan adam mai yada shirye-shirye cikin harshen Hausa a Arewacin Najeriya.

Farar Tattabara Official Logo

Farar Tattabara (White Dove) Wata Cibiyar Isar da Saƙo na Musamman a Arewacin Najeriya

Shirin Madubi Logo

Gina wani Tallafi na kafar Watsa Labarai don daukar matakan kulawa da Al'amuran Al'umma
(SMSCAM)

Tambarin Fasaha A Rayuwar Iyali

Cike gibin
Dake tsakanin Jinsi a fannin Fasaha
Fasaha a Rayuwar Iyali

MATSAYAR MU

Tare da samun kaiwa ga adadin masu sauraro sama da miliyan 15, shirye-shiryen rediyo na EAI; Ina Mafita, Ilimi Abun Nema, Labarin Aisha, Madubi da kuma Fasaha a Rayuwar Iyali suna karfafawa ga sabon karni na ababen koyi da kuma sanar da sako da ke aiki tukuru don ganin rayuwar iyalan su da ta al’umomin Arewacin Najeriya ta inganta.

SHAFUKAN MU

Masu sauroronmu

Tare da wadatar masu sauraron sama da miliyan 15, shirye-shiryen rediyo na EAI-Nigeria; Ina Mafita, Ilimi Abun Nema, Labarin Aisha, Madubi da Fasaha A Rayuwar Iyali ...

Kara karantawa

Ku nuna Goyan bayanku!

Domin kowacce tambaya, ko korafi

Tuntube mu

Lambar tarho

234 8099000696
234 9080818484

Emel

farartattabara@gmail.com
humanresourceng@equalaccess.org

Najeriya

Abuja: Wuse 2 Abuja, Nigeria.
Kano: Nassarawa GRA, Kano, Nigeria.

Amurka

1001 Connecticut, Ave, NW, Suite 909, Washington DC, 20036 USA.

Cike dukkanin bayananka anan

Zamu Tuntubeka

×